1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Myanmar an tarwatsa masu bore

Abdoulaye Mamane Amadou
February 27, 2021

'Yan sanda a Rangoun na Myanmar sun yi amfani da harsashen roba don tarwatsa masu boren kin jinin gwamnatin mulkin soja da suka fito yin zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/3q0Yu
Myanmar Yangon  Proteste Putsch Polizei
Hoto: Ye Aung Thu/AFP

Rahotanni sun ce tun daga farko 'yan kalibar Mon ne suka fito yin bikin ranar Mon ta shekara shekara kafin daga bisani sauran tsirarun kabilun kasar su halarci wurin, kuma nan take shagalin bikin ya rikida ya koma tarzomar kin jinin gwamnati, lamarin da ya kai ga jami'an tsaro suka tarwatsasu.

Ko a ranar Juma'ar da tagabata, an shafe tsawon sa'o'i ana dauki ba dadi tsakanin 'yan sanda da masu zanga zanga, a kasar ta Myanmar da ke ci gaba da fuskantar bore tun bayan hambarar da mulkin shugaba Aung San Suu Kyi da sojoji suka yi a farkon watan Febrairun wannan shekara.