An yi bukin ratsad da sabon Firaministan Japan a birnin Tokyo
September 26, 2007Talla
An rantsad da sabon FM Japan Yasuo Fukuda a wani buki da aka yi a birnin Tokyo. Fukuda ya yi alkawarin sake daga mutuncin ´yan siyasa a idanun jama´a sannan ya ce zai hada kai da masu adawa da shirin kara wa´adin sojojin ruwan Japan a cikin rundunar kasa da kasa a Afghanistan. Fukuda mai shekaru 71 ya yi kaurin suna wajen sasantawa da ´yan adawa kuma ana daukar sa a matsayin shugaban da Japan ke bukata a yanzu bayan dambaruwar siyasa da ta yi da ita karakshin tsohon FM Shinzo Abe wanda ba zato ba tsammani ya yi murabus makonni biyu da suka wuce. A wani lokaci yau Fukuda da sauran ministocin sa zasu yi ganawarsu ta farko.