Afirka ta kasa kai labari a gasar U17
November 11, 2019Za mu dauka shirin da gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka ta matasa 'yan kasa da shekaru 17 da ke wakana a kasar Brazil, inda yanzu a ka yi waje da illahirin wakillan nahiyar Afirka guda hudu wato Kamaru wacce aka kora tun a zagayen farko da Angola da Najeriya da Senegal a wasan zagaye na biyu. A takaice dai babu wakilin Afirka daya da ya kai wasan kwata final na gasar. A yanzu dai kasar Hollande wacce ta doke Paragay da ci 4-1 a wasan kwata Final da kuma da kuma Mexico wacce ta doke koriya ta Kudu da ci daya da banza a wasan kwata Final sun yi nasarar zuwa wasan kusa da na karshe. A ci gaban wasannin na kwata final Faransa za ta fafata a daren wannan Litinin da Spain a yayin da a gobe Talata Italiya za ta kara da Brazil.
1. Bundesliga
A wasanin lig na Jamus na Bundesliga yayin wasannin karshen mako: Schalke da Düsseldorf sun tashi 3 da 3, kana Mönchengladbach ta doke Werder Bremen 3 da 1, sannan Freiburg ta doke Eintracht Frankfurt 1 da nema. Ita ma Leverkusen ta bi Wolfsburg gida ta doke ta 2 da nema. A nata bangaren Bayern Munich ta doke Borussia Dortmund 4 da nema. Ita kuwa Hertha Berlin ta sha kaye a gida a hannu kungiyar Leipzig na ci 4 da biyu.
Ita dai Mönchengladbach ke jagorancin teburin na Bundesliga na Jamus da maki 25, sannan Leipzig mai maki 21 tana matsayi na biyu, haka ita ma Bayern Munich da maki 21 tana matsayi na uku, Freiburg ita ma da makin 21 tana matsayi na hud 4 inda kwallaye kadai ya raba tsakanin kungiyoyin na biyu, uku, da hudu.
2. Premiya Lig:
A wasannin Premier lig na Ingila da aka kara Leicester ta doke Arsenal 2 da nema, sannan Manchester United ta samu galaba kan kungiyar Brighton 3 da 1, haka ita ma Liverpool ta doke Manchester City 3 da 1, yayin da Newcastle ta samu nasara kan Bounemouth 2 da 1.
Zuwa yanzu Liverpool ke jagoranci teburin na Premier lig na Ingila da maki 34, yayin Leicester ke matsayi na biyu da maki 26, ita kuma Chelsea da makin 26 ita ma tana matsayi na uku, sannan Manchester City da maki 25 tana matsayi na hudu.
3. La Liga:
A wasannin La Liga na Spain da aka kara Sevilla ta bi Betis har gida ta doke ta 2 da 1. Mallorcar ta doke Villareal 3 da 1, ita ma Atletico Madrid ta doke Espanyol 3 da 1.
Kawo yanzu Barcelona ke jagorancin teburin na La Liga a Spain da maki 25, yayin da Real Madrid le matsayi na biyu da maki ita ma 25. Sannan Atletico Madrid mai maki 24 tana mataki na uku.
Kwallon Tenis ta tebur a Nijar:
A jamhuriyar Nijer , wasar kwallon tenis ta kan tebur ta samu karbuwa sannu a hankali daga cikin al'umma duba da yadda a cikin 'yan shekarun baya-bayan nan aka fara shigo da ita a sauran yankunan kasar sabanin gurbin da aka yi mata a manyan birane ko kuma ganin ta da ake yi a TV kawai .
Wakilinmu Issuhu Maman na jihar tahoua daya daga cikin yankunan da wasar ke tashe a yanzu ya ziyarci gurin da ake yin ta ga kuma rahoton da ya aiko muna.