An zargi sojin Burkina Faso da kisan jama'a
May 21, 2018Kungiyar Human Right Watch ta zargi sojojin kasar Burkina Faso da kisa da kuma azabtar da mutanen da suka kama a bisa zargi da kasancewa 'yan ta'adda a lokuttan da suke aiwatar da sintirin yaki da 'yan ta'addanci a kasar.
Cikin wata sanarwa da daraktar Kungiyar ta HRW reshen Sahel Corinne Dufka ta fitar, ta ambato wasu shaidun gani da ido na cewa sun shaida lokacin da sojojin gwamnatin Burkina Faso suka bindige wasu mutanen akalla 14, da kuma wasu mutanen na daban guda hudu da suka rasu a sakamakon azabar da sojojin suka gana masu a inda suke tsare da su.
Wasu shaidun da dama a cewa Kungiyar ta HRW sun ce sun sha tsintar gawarwakin mutane wadanda aka rufe fuskokinsu da kyalle hannuwansu a daure a yadde a bakin hanya.
Kungiyar ta HRW ta ce masu garuruwa da yawa sun shaida mata cewa akwai mutanen da ba su ji ba su gani ba wadanda sojojin suka yi katarin kamasu a kusa da wuraren da 'yan ta'adda suka kai wani hari kana suka kashe su ba tare da wani bincike ba. Ministan tsaron kasar ta Burkina Faso Jean Claude Bouda ya bayyana cewa gwamnati a shirye take ta gudanar da bincike a kan wannan lamari.