1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi sojojin Burkina da kashe-kashe

Mouhamadou Awal Balarabe
March 14, 2019

Kungiyar MBDHP ta ce dakarun Burkina Fasu sun yi wa mutane 60 kisan gilla a watan Fabrairu da sunan yaki da ayyukan ta'addanci, lamarin da gwamnatin kasar ta ce za ta zurfafa bincike a kai don gano gaskiyar lamarin.

https://p.dw.com/p/3F50L
Afrika Burkina Faso  l Militär l Nigerianische Armee
Hoto: DW/F. Muvunyi

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Burkina Faso da ake yi wa lakabi da MBDHP ta bayyana cewa sojojin kasar sun yi wa akalla mutane 60 kisan gilla a watan Fabrairu da sunan yaki da ayyukan ta'addanci. Sai dai cikin wata sanarwa da ta fitar a birnin Ouagadougou, gwamnatin kasar ta ce kotun soji ta fara gudanar da bincike kan wadannan zarge-zargen cin zarafi.

 A farkon watan Fabrairun ne dakarun Burkina Faso suka kaddamar da hare-hare a arewacin kasar a kan 'yan jihadi a matsayin ramuwar gayya, inda suka yi ikirarin kashe masu fafutuka da makamai 146. Sai dai kungiyar ta kare hakkin bil Adama ta ce mafi yawan mutanen da sojojin suka kashe Fulani ne makiyaya bisa ga sahihan bayanai da ta samu.

 Ita dai  Burkina Faso ta shafe shekaru hudu tana fuskantar hare-haren ta'addanci, wadanda suki yi sanadin mutuwar fiye da mutane 300. Kungiyoyin jihadi goma sha biyu ne suke matsa kaimi a kasar ciki har da Ansarul Islam, a cewar kungiyar kasa da kasa ta International Crisis Group.