Ana cikin hali na ɗarɗar dangane da tashar nukiliyar Japan
March 12, 2011A haƙiƙa dai matsalar tana tattare da barazanar gaske, kamar yadda aka ji daga wani mai magana da yawun gwamnatin ƙasar Japan. Mutane da cikin hali na ɗimuwa da rashin sanin tabbas. Rahotanni dai sun nuna cewar wani ɓangare na tashar makamashin nukiliyar ya rushe sakamakon wata bindigar da aka fuskanta a cikin ginin ana kuma fargabar fuskantar wani haɗari irin shigen wanda ya wakana a Chernobyl ta tsofuwar tarayyar Soviet shekaru ashirin da biyar da suka wuce. A tashar ta Fukushima a ƙasar Japan tsarin tsaron da aka tanadar ya taɓarɓare ne sakamakon ɗaukewar wutar lantarki gaba ɗaya da aka fuskanta bayan girgizar ƙasar. A cikin hira da aka yi da shi ta gidan telebijin Michael Sailer, ƙwararren masani akan al'amuran nukiliya nuni yayi da cewar:
Hatsarin nukiliyar ba ya da magani in har ya samu
"Da wuya a samu kafar shawo kan irin wannan matsala, kuma a sakamakon haka ne ake tanadar da tsaro a tashoshin makamashin nukiliyar domin kaucewa daga irin wannan mawuyacin hali, wanda in har ya samu to kuwa tsarin ba zai taimaka ba. Ana iya yin bakin ƙoƙari wajen ɗaukar wasu matakai na lafar da raɗaɗin zafin tashar ta yadda za a ƙayyade yawan dussar nukiliyar dake yaɗuwa. Amma in banda hakan ba wani matakin da za a iya ɗauka na dakatar da wannan ƙaddara."
Ita dai tashar makamashin nukiliyar ta Fukushima Daiichi ta ɗaya tana amfani ne da tafasasshen ruwa,wanda wani injin mai farfela ke sarrafawa domin samar da wutar lantarki. To sai dai kuma idan an fuskanci bindiga a tashar raɗaɗin zafin kan ƙaru fiye da kima ta yadda a ƙarshe tashar gaba ɗayanta zata yi bindiga kamar yadda lamarin ya kasance dangane da tashar Chenobyl shekaru ashirin da biyar da suka wuce. To ko me zai iya biyowa baya. An ji daga bakin Dr. Sebastian Pflugbeil, wanda ya kasance cikin tawagar da suka binciki hatsarin na Chernobyl yana mai bayanin cewar:
Ga alamu ba za a fukanci hatsari irin na Chernobyl ba
"Abin da zai faru shi ne tulun-ruwan tashar zai lalace kuma dussar nukiliya ta samu kafar yaɗuwa a cikin iska. Mai yiwuwa ba zata ci gaba da ƙuna ba ta yadda dussar ba zata yi nisan kilomita goma a samaniya ba ballantana ta rutsa da wasu yankuna. Amma matsalar dake akwai ita ce mai yiwuwa dussar ta yaɗu da yawa a wani yanki mai faɗin murabba'in kilomita ɗari biyar. Hakan ba shakka zata yi mummunar ɓarna ga jama'a a ƙasar ta Japan."
A kuma halin da ake ciki yanzu masu adawa da tashoshin nukiliya a nan Jamus sun shiga zanga-zanga da yin kira ga gwamnati da ta dakatar da ayyukan tashoshin nukiliyar ƙasar, a yayinda ita kuma shugabar gwamnati Angela Merkel ta kira taron gangami na 'yan Christian Union don tattauna matsalar.
A ƙasa za'a iya sauraron sautin rahoto akan hatsarin tashoshin nukiliya da kuma wani rahoton akan ƙoƙarin shawo kan matsalar Nukliya a ƙasar Japan.
Mawallafi: Sybille Golte/Ahmad Tijani Lawal
Edita: Abdurrahaman Hassane