1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana fama da zafi mai tsanani a Turai

June 19, 2022

Kasashen nahiyar Turai sun shiga wani yanayi na zafi mai tsanani wanda ke jefa rayuwar jama'a cikin matsala. Yanayin dai ya zarta yadda aka saba gani a baya.

https://p.dw.com/p/4CuA2
Spanien Hitzewelle im Juni BG
Hoto: Paul White/AP/picture alliance

Kasashen Faransa da Spaniya da ma wasu na gabashin nahiyar Turai sun shiga yanayi na zafi mai tsanani a 'yan kwanakin da ake ciki, inda a wasu yankunan ma aka soma ganin ibtila'in gobarar daji.

Zafin da ya haura maki 40 a wasu kasashen, masana sun yi hasashen samun hakan cikin wannan wata na Yuni.

Gobarar dajin ta yi barna musamman a yankin Kataloniya na kasar Spaniya.

Yanayin na zafi dai ba sabon abu ba ne a kasashen na Turai duk da yawan sanyi da ake da shi, to sai dai a wannan karon sun danganta shi da matsalar dumamar yanayi.