Dokar hukuncin kisa ta ragu a duniya
September 7, 2018Talla
Sai dai kungiyar ta ce har yanzu zartas da hukunci mai tsauri na ci gaba da zama babbar barazana ga hakkin dan Adam, inda kasar China ke zama kan gaba cikin kasashen duniya 23 masu aiwatar da tsauraran hukunci kan wadan da aka samu da aikata laifuka.
A karshen shekarar 2017 kasashen 142 ne suka soke dokar hukunci kisa kan wasu laifuka, yayin da kasashe 106 suka yi watsi da hukuncin kisa kan manyan laifukan.
Kasahen Afirka da ke Kudu da Sahara na cikin kasashen da aka samu ci gaba na yin watsi da hukuncin kisa, inda kasashen Burkina Faso da Chadi da Kenya da Gambiya ke daukar matakan dakatar da hukuncin kisan ta hayar kafa sabbin dokoki. Sai dai dokar na ci gaba da tasiri a kasashen Somaliya da Sudan ta Kudu.