1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin Mahamadou Issoufou da laifin cin amanar kasa

Gazali Abdou Tasawa RGB
September 19, 2022

Kawancen kungiyoyin farar hula na M62 na son Shugaba Mohamed Bazoum ya binciki tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou kan zargin cin amanar kasa.

https://p.dw.com/p/4H4Rx
Demokratische Republik Kongo Kinshasa | Nigerianischer Präsidenten Mahamadou Issoufou
Mahamadou IssoufouHoto: Presidence RDC/G. Kusema

Kawancen kungiyoyin farar hula na M62 a jamhuriyar Nijar ne suka yi kira ga gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum da ta gurfanar da Mahamadou Issoufou a gaban kuliya a bisa zarginsa da cin amanar kasa, kan batun kwangilar shimfida layin dogo da ma girke sojojin ketare a kasar.

Kawancen kungiyoyin na M62 wanda ya kunshi kungiyoyin farar hula da na kwadago, ya yi wannan kira ne a cikin wata sanarwar da ya fitar a taron gangamin da ya shirya a karshen makon da ya gabata. Kawancen na zargin tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou da cin amanar kasa ta hanyar girke sojojin ketare a kasar ba da izinin majalisa ba, da kuma bai wa kamfanin Bolore na Faransa kwangilar shimfida layin dogo daga Yamai zuwa Dosso ba a kan ka’ida ba.

Tuni dai wannan batu ya haifar da sabani a tsakanin sauran kungiyoyin farar hula wadanda ba sa cikin kawancen na M62. Kawancen na M62 ya ce, idan har mahukuntan Nijar ba su gurfanar da tsohon shugaban kasar Alhaji Mahamadou Issoufou a gaban kuliya ba, to a shirye suke su shigar da karansa a gaban wata kotun kasa da kasa domin cimma burinsu.