1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Anobar ƙyanda a Somaliya

June 10, 2014

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewar dubban yara kanana a Somaliya na fuskantar barazanar mutuwa ko samun nakasa saboda anobar cutar ƙyanda.

https://p.dw.com/p/1CGCf
Somalia Vertriebenenlager Darwisch in Mogadischu
Hoto: Bettina Rühl

A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa wadda asusun kula yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya, wato UNICEF, da kuma Ƙungiyar Lafiya ta Duniya, WHO, suka bayyana sun ce cutar ta riɓanya har sau huɗu, fiye da shekarar bara, don haka suka ce a kwai buƙatar a gaggauta yin wani kampe na yin alurar riga kafi domin kaucewa bala'in.

Wannan sanarwa ta zo ne a lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta ba da rahoton cewar akwai babbar barazana ta ƙaranci abinci a kasar, bayan yunwar da aka yi fama da ita shekaru uku da suka wucce saboda rashin samun saukar ruwan sama da kuma yaƙin da ake yi a ƙasar.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Suleiman Babayo