1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU ta dakatar da Burkina Faso daga cikin kungiyar

Gazali Abdou TasawaSeptember 19, 2015

Kungiyar Tarayyar Afrika ta AU ta dakatar da Burkina Faso daga cikin kungiyar a wani mataki na nuna adawa ga juyin mulkin da sojojin kasar suka kaddamar a kasar a tsakiyar wannan mako.

https://p.dw.com/p/1GYzV
Neuer Hauptsitz der Afrikanischen Union in Addis Abbeba
Hoto: Imago

Kungiyar Tarayyar Afrika ta AU ta dakatar da kasar Burkina Faso daga cikin kungiyar a wani mataki na nuna adawa ga juyin milkin da sojojin kasar suka kaddamar a kasar a tsakiyar wannan mako. Shugaban komitin zartarwar kungiyar ta AU Mull Katende ya sanar da daukar wannan mataki a wannan Juma'a da ta gabata lokacin wani taron manema labarai da ya kira jim kadan bayan kammala wani taron gaggawa da kungiyar ta shirya a cibiyarta da ke a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Ko baya ga dakatar da kasar ta Burkina Faso, kungiyar ta AU ta kuma dauki matakin haramta wa illahirin mambobin sabuwar hukumar mulkin sojan kasar yin balaguro, dama izinin taba kudaden ajiyarsu na bankunan a duk kasashen nahiyar.