AU ta jinjinawa Burkina Faso
November 18, 2014Talla
AU ɗin ta ce ta kuma jingine dukanni wani shiri da ta ke na maida Burkina Faso ɗin saniyar ware a tsakanin ƙasashen ƙungiyar tunda dai masu ruwa da tsaki a ƙasar sun kai ga tabbatar da farar hula da zai riƙe madafun iko a matsayi na rikon kwarya.
Shugaban riƙon ƙwaryar dai Michel Kafando wanda tsohon jami'in diflomasiyya ne ya sha rantsuwar kama aiki a Talatar nan inda ya lashi takobin ɗorewar tsarin mulkin farar hula a ƙasar.
A gobe Laraba nan ce ma ake sa ran zai bayyana sunan firaministan da zai yi aiki tare da shi wanda za su hada gwiwa wajen fidda mutane 25 da za su yi aiki a majalisar ministocin ƙasar.