1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nahiyar Afirka na fuskantar bullar sabon nau'in corona

Ramatu Garba Baba
July 1, 2021

Daga cikin al'ummar nahiyar Afirka da suka zarta biliyan daya, kashi daya cikin dari kacal aka yi ma allurar rigakafin cutar corona inji Kungiyar tarayyar Afirka.

https://p.dw.com/p/3vsyI
Madagascar Covax
Hoto: Mamyrael/AFP

Wakilin Kungiyar tarayyar Afirka ya ce nahiyar na cikin tsaka mai wuya na rashin allurar riga-kafin cutar corona a daidai lokacin da kasashen yankin ke fuskantar barazanar bullar kashi na uku na wani sabon na'uin annobar.

Wakilin Mista Strive Masiyiwa, ya zargi Turai da jan kafa wajen cika alkawuran yin raba daidai na rigakafin a karkashin shirin nan na COVAX na tallafawa kasashe marasa karfi da rigakafin cutar. 

Ya ce, an tsara cewa Afirka za ta karbi allurar kimanin miliyan 700 kafin watan Disamban wannan shekara da muke ciki, amma kawo yanzu, allurar miliyan sittin da biyar aka samu, wannan na nufin kashi daya kacal cikin dari na al'ummar nahiyar kadai aka yi ma rigakafin cutar.

Nahiyar mai al'umma sama da biliyan daya na fuskantar barazanar yaduwar sabon na'uin na corona da aka ce na tattare da hadarin gaske ga dan adam. Matsalar da aka fuskanta, ba ta rasa nasaba da kin cika alkawura na tallafin kudin coronar da wasu daga cikin kasashen Turan suka dauka.