AU ta tura ƙarin sojoji zuwa Somaliya
August 23, 2010Sojojin wanzar da zaman lafiya a ƙarƙashin lemar Ƙungiyar Gamayyar Afirka(AU) sun isa Mogadishu babban birnin ƙasar Somaliya. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato wani jami'in ƙungiyar ta AU da ya tabbatar da isan ɗaruruwan sojojin a Mogadishu yana cewa sojojin sun fito ne daga Uganda. A watan jiya ne dai Uganda ta yi alƙawarin ƙara yawan sojojinta zuwa dubu 2 a Somaliya, bayan harin da ƙungiyar al-Shabaab ta kai Kampala wanda ya kashe mutane 70.Tun a shekara ta 2007 ne dai ƙungiyar al-Shabaab mai alaƙa da ƙungiyar al-Ƙa'ida ke yaƙi da gwamnatin riƙon ƙwaryar Somaliya. A taron shugabannin ƙungiyar AU da aka gudanar a birnin Kampala na Uganda, AU ta sha alwashin ƙara yawan sojojinta´domin tabbatar da tsaro a Somaliya.
Mawallafi: Babangida Jibril
Edita Halima Balaraba Abbas