1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aung San Suu Kyi ta yi jawabi a kan batun Rohingya

Salissou Boukari AH
September 19, 2017

Gabanin taron Majalisar Dinkin duniya a birnin New York, jagorar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi ta yi jawabi a karo na farko ga al’ummar kasar kan halin da ake ciki da rikicin Musulmin kasar 'yan kabilar Rohingya.

https://p.dw.com/p/2kHom
Myanmar Aung San Suu Kyi
Hoto: Getty Images/AFP/Ye Aung Thu

Jawabin na Aung San Suu Kyi dai zuwa ga ‚yan kasar na Myanmar, ta yi shi ne kuma  zuwa ga kasashen duniya inda a halin yanzu wannan batu na 'yan Rohingya ya zamanto babban abin da ke daukan hankalin al'umma. Bayan da ta kudiri aniyar kauracewa taron na Majalisar Dinkin Duniya, shugabar gwamnatin ta dauki magana daga birnin Naypyidaw fadar gwamnatin gasar ta Bama a yayin da ta ke shan suka daga bangarori daban-daban na duniya. Sakamakon yadda a baya ta yi gum da bakinta  ake cin zarafin tsirarun kasar 'yan Rohingya da a halin yanzu fiye da dubu 400 suka ketara zuwa kasar Bangladesh. Sai dai Aung San Suu Kyi mai rike da takardar yabo ta Nobel na zaman lafiya wadda kuma ta nuna cikeken goyon bayanta kan abubuwan da sojojin kasar ke yi, ta sassauto a cikin jawabin da ta yi.

'Yan Rohingya suna cikin tasku

"Muna masu Allah wadai da duk wani nau'i na take hakin dan Adam, da kuma wasu halaye da ba sa bisa kan ka'ida ba. Mun kasance masu ba da kai wajen ganin lamurra sun daidaitu, samun zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da bin hanyoyin doka a dukkan fadin kasar." Ga baki dayan al'ummar kasar ta Myanmar dai na shan suka ne daga kasashen duniya kan makomar tsirarun 'yan Rohingyas da a suka kai adadin dubu 420 da ke gudun hijira a kasar Bangladesh, inda ma kasashen na duniya har ma da majalisar Dinkin Duniya suka kalli matakin na hukumomin na Myanmar a matsayin wani yunkuri na kawar da wannan al'umma daga doron kasa.