Babban Sakataran MDD ya yi kiran da a samar da zaman lafiya a Somaliya
December 9, 2011Talla
Babban sakataran Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya ziyarci birnin Mogadishiyu a wani ran gandi na ba zata da ya soma a ƙasar Somaliya .Ziyara wacce ita ce irin ta ta farko da wani sakataran Majalisar ta ɗinkin duniyar ke yi a ƙasar tun a shekara ta 1993.
Na da zumar lura da halin da jama'ar ƙasar suke ciki bayan farin da aka yi fama da shi wanda ya hadasa yunwa a yankin kusuRwar Afrika.Da yake yi magana da manema labarai sakataran Majalisar ta Ɗinkin Duniya ya yi kira ga yan ƙungiyar Al Shabab da su bada hadin kai ga shirin samar da zaman lafiya tare da kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a ƙasar.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu