1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban taron jam´iyar CDU a birnin Hannover

December 12, 2007

Jam´iyar ta zayyana sabbin manufofinta

https://p.dw.com/p/Cafh
Shugabannin CDUHoto: AP

Masu sauraro barkanmu da warhaka. Barkanmu da sake saduwa a cikin shirin Mu Kewaya Turai, wanda ya saba kawo muku nazari akan manufofi na siyasa da tattalin arziki da zamantakewa hade da dangantakar ƙasashen Turai.

A makon da ya gabata ne jam’iyyar CDU mai mulkin hadin guiwa da SPD a nan Jamus ta kammala babban taronta a garin Hannover, inda ta zayyana sabbin manufofin ta. Bayan manufofin ta na shekarun 1978 da 1994, a karo na uku jam´iyar ta shugabar gwmanatin Jamus Angela Merkel ta gabatar da sabbin manufofin ta. Bayan zazzafar muhawwara wakilai 1001 suka amince da sabon kudurin jam´yiar yayin da biyu suka yi rowar kuri´un su a gun babban taron na birnin Hannover. Shugabannin jam´iyar ta CDU na masu ra´ayin cewa za´a yi shekaru 15 zuwa 20 jam´iyar na bin waɗannan manufofi. To shirin Mu Kewaya Turai na wannan mako zai duba yadda ta kaya ne a taron na birnin Hannover. Masu sauraro Mohammad Nasiru Awal ke marhabin da saduiwa da ku a wannan lokaci.

A ƙarshen babban taron na jam´iyar CDU a birnin Hannover an ga wata alama ta rashin jituwa tsakanin jam´iar CDU da SPD musamman a dangane da yakin neman zabe a shekara ta 2008 da ta 2009. shugabannin CDU da SGJ Angela Merkel sun kira da a tashi tsayin daka don yakar abokiyar ƙawancenta ta birnin Berlin tare da kashe zaɓen ´yan majalisun dokokin jihohin Lower Saxony da Hesse da kuma birnin Hamburg.

Kwana guda gabanin kammala taron CDU ta bayyana kan ta a matsayin wata jam´iyar tsakiya ta talakawa. Jam´iyar ta kuma nesanta kanta daga manufofin irin na jam´iyar SPD. Jam´iyun adawa ciki har da jam´iyar SPD sun yi suka dangane da kwarya-kwaryar sakamakon da aka samu a babban taron na CDU. Suka ce surutu kaɗai aka yi ba tare da fayyace wata sahihiyar alƙibla ba.

To sai dai Angela Merkel ta nuna gamsuwa da sakamakon taron a lakaci da take yiwa wakilai sama da dubu ɗaya jawabin bankwana. Jim kaɗan gabanin haka, wakilan jam´iyar sun amince da wani ƙuduri a dangane makomar jam´iyar mai taken A yi tunani mai zurfi a manufofin siyasa na karni na 21. A fakaice wannan ƙuduri na da manufa irin ta sakarwa harkokin kasuwanci mara wadda gwamnatin CDU bayan yaƙin duniya ta yi amfani da ita wajen sake gina tarayyar Jamus. Wannan manufar ta haɓaka harkokin kasuwanci ta hada da duba bukatun al´uma kamar yadda Angela Merkel ta nunar a jawabin rufe taron.

Merkel ta ce:

“Jami´yar CDU jam´iya ce da take bin manufofin sakarwa harkokin kasuwanci mara tare da duba bukatun al´uma. Zamu ci-gaba da bin wannan manufa musamman a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa da suka shafi harkokin kasuwanci.”

Ƙudurin da aka amince da shi a babban taron na birnin Hannover wani yunƙuri na farko na zayyana yadda harkokin kasuwancin kasa da ƙasa su ke inji firimiyan jihar Hesse Roland Koch. Hakan na zaman wani sharadi ga masu zuba jari a ko-ina cikin duniya kamar yadda kungiyar cinikaiya ta duniya ke ƙoƙarin yi amma a aikace ba a aiwatar da shi, inji Koch. Abu mafi dacewa shi ne sa ido kan hadar hadar kudi tsakanin kasa da kasa. Ya kamata a dauki sahihan matakan rigakafin aukuwar matsaloli ga tattalin arzikin duniya kamar yadda ake fuskanta a kasuwannin sayar da gidaje a Amirka. Koch ya ce abu mafi muhimmanci shi ne sa ido kan kamfanonin ketare masu zuba jari.

Koch ya ce:

“Kamfanin samar da Gas na Rasha wato Gazprom kamfani ne da ke ƙarƙashin gwamnatin Rasha. Ba dole ne a soki lamirinsa. Ba dole ne a rushe wannan kamfani ba. To amma idan wannan kamfani ya sai hannun jari, kamar fadar Kremlin ce ta saye jarin. Saboda haka ya dole a bawa duk wata gwamnatin da Kremlin ta saye jari a cikin kasarta, damar yanke shawara ko ta na bukatar jarin daga Kremlin ko kuma a´a.”

Koch ya kuma yi kashedi cewa watan wata rana kamnfanoni da hukumomi ke juya akalarsu wato kamar daga kasashen Rasha da China da kuma kamfanino hakan man fetir zasu kasance masu rinjaye a fannin tattalin arzikin duniya.

Koch ya ce:

“Tun a yanzu ya kamata mu nuna musu matsayin mu, domin in mun jira zuwa wasu shekaru nan gaba, to zamu makara. Saboda haka yake da muhimmanci tun yanzu a yi magana dangane da ka´idojin hulɗar kasuwanci ta kasa da kasa.”

A dangane da haka babban taron ya yi kira ga Angela Merkel da ta gaggauta kafa dokoki bisa wadannan shawarwari. Bugu da ƙari ta kuma samu ƙarin goyon baya a jam´iyar inda ba ta da wani mai gogayya da ita.

A dangane da zabukan da ke tafe a badi Merkel ta yi kira ga ´ya´yan jam´iyar da su tashi tsaye su mayar da himma don ganin jam´iyar ta yi nasara. Ta ce dole ne su bazu akan tituna don faɗakar da jama a manufofin jam´iyar CDU.

Merkel ta ce:

“Dole ne mu yi nasara a zabukan majalisun dokokin jihohin, domin ta haka za´a tabbatar da jin dadin mutanen wadannan jihohi. Rayuwar mazauna jihohin da jam´iyun hadin guiwa na CDU da CSU ke mulki, ta inganta ƙwarai da gaske.”

Shi ma a nasa ɓangaren shugaban jam´iyar CSU mai kawance da jam´iar CDU, Erwin Huber cewa ya yi yanzu lokaci yayi da ya kamata a juyawa jam´iyar SPD baya.

Huber ya ce:

“Abu ɗaya da ya haɗa kan masu ra´ayin canji shi ne mulki. Saboda haka bai kamata mu amince da jam´iyar SPD ba. Duk mutumin da yayi kokarin saka manufar gurguzu cikin yakin neman zabe kamar Mista Beck, to lale yana da alaƙa da ´yan kwaminis.”