An bankado almundahana da kudin manoma a Nijar
January 2, 2023Yanzu haka dai hukumomin shari'a na kasar ta Nijar kame wasu daga cikin manyan jami'an bankin da suka hada da Babban Daraktansa. Tuni kuma kungiyoyin manoma da ma na kungiyoyin kare hakkin dan adam na kasar ta Nijar suka soma bayyana gamsuwarsu da matakin.
Hukumar CENTIF wacce ke fafutikar yaki da wanke kudaden haram da kuma samar da kudaden shiga ga kungiyoyin ‘yan ta'adda a kasar ta Nijar ce ta bankado wannan almundahana ta kudi kimanin miliyan dubu biyar na CFA a Bankin manoma na BAGRI.
Wasu bayanai sun nunar da cewa yanzu haka akwai wasu manyan jami'an banki da suka hada da babban daraktansa da suka shiga hannun hukumar 'yan sandan farin kaya, wacce ke ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin. Da ya ke tsokaci kan wannan lamari, Malam Abdou Neino Gajango shugaban kungiyar matan karkara ta FENAF ya bayyana farin cikinsa da kamen jami'an bankin.
Yanzu haka dai wannan banki na BAGRI na neman durkushewa a sakamakon kariyar jarinsa. Kuma kungiyar transparency International reshen kasar Nijar a ta bakin shugabanta Malam Maman Wada na ganin ga labarin da suke da kan barnar da aka aikata a wannan banki, kunnuwan ne aka gani jakunan na a baya.
Daga nata bangare kungiyar Mojen wacce ke fafautikar kare hakin dan Adam a Nijar ta bakin shugabanta Malam Siraji Issa, cewa ta yi sannu a hankali alkawarin a shugaban kasa Mohamed Bazoum ya dauka na yakar cin hanci a kasar ya soma tabbata a kasa.
A shekara ta 2011 ne dai gwamnatin ta kafa wannan banki na BAGRI da nufin tallafa wa manoma, da makiyaya da sauran mazauna karkara ta hanyar ba su bashi. Sai dai manoma da dama na cewa shekaru 11 kenan da bankin ke ce masu su gafara gas a amma har kawo yanzu ba su ga ko da kaho ba.