Bala'in fari a Somaliya
February 8, 2016Talla
A wani rahoton da MDD ta fitar yau Litinin 08.02.2016, tace sakamakon tsananin fari da aka yi, a yanzu kasar da yaki ya dai-daita, akwai wani bala'i da ke fisaknatarsu. A cewar rahoto tsananin rashin abinci mai gina jiki musamman ga yara kanana, a yanzu ya kai wani mizani na tada hankali. Inda yanzu yara sama da dubu 30 ke fama da bakar yunwa. Bisa kiyasin MDD, Somaliyawa miliyan hudu da dari bakwai, wato kashi arba'in na al'ummar kasar suna matukar bukatar tallafin abinci.