Bala'in girgizar ƙasa a arewacin Japan
March 11, 2011Girgizar ƙasa da ƙarfinta ya kai maki takwas da ɗigo tara a ma'aunin Richter ta haddasa hasarar kadarori da kuma rayukan mutane da dama a arewacin Japan. Wannan bala'in shi ne mafi muni da ƙasar ta fiskanta a cikin shekaru 140 na baya-bayannan. Ya zuwa yanzu dai mutane 90 ne aka tabbatar cewa sun rigamu gidan gaskiya yayin da wasu da dama kuma suka ɓace. Igiyar ruwan Tsunami da ta biyo bayan girgizar ƙasar ta yi awan gaba da wani jirgin ruwa da ke maƙare da fasinjoji sama da 100. Kana ta na ci gaba da barazana da rayukan mazauna yankin arewa maso arewacin kƙasar ta Japan, da ma dai sauran ƙasashe da ke maƙwabtaka da ita.
Hukumomin ƙasar ta Japan sun rufe filin tashi da kuma saukan jirage na birnin Tokyo, tare da rufe matatan man Ichihira, a wani matakin na taƙayta zirga zirga da asarar rayuka. Mutane miliyon huɗu na ƙasar ta Japan na cikin duhu sakamakon katsewar wutan lantarki da bala'in ya haifar. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya nuna jiyayi game da bala'in da kasar ta Japan ta fiskanta.
"Ina so in gabatar da ta'aziya ta ga 'yan uwan waɗanda suka rigamu gidan gaskiya. Ina so kuma in yi amfani da wannan dama wajen nuna juyayi ga waɗanda suka ji rauni. Ba mu san yawan mutane da suka rasu ya zuwa yanzu ba. Amma kuma muna jajantan wa gwamnatin Japan game da abin da ya afku. Wannan bala'i na girgizar ƙasa ya jefa gwamnatin Japan cikin wani mawuyacin hali."
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal