An kai harin bam Somaliya
May 24, 2020Talla
Mutane biyar sun rasa rayukansu yayin da wasu sama da 20 suka jikata a wani harin bam da ya tashi a garin Baidoa da ke yamma da birnin Magadishu fadar gwamnatin kasar Somalia a yayin da suke shagulgulan bikin karamar sallah.
Wani jami'in 'yan sanda da ke yankin Mohamed Muktar ya tabbatar da faruwan lamarin ga kamfanin dillancin labarai na Faransa na AFP.