1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bam ya kashe mutane 20 a Somaliya

Abdul-raheem Hassan
October 14, 2017

Akalla mutane 20 sun mutu a wani harin bam da ya tarwatse a cikin wata babbar mota a tsakiyar birnin Mogadishu, harin ya rugurguza wani bangare na wani makeken Otal da ke kusa da ma'aikatar harkokin wajen kasar.

https://p.dw.com/p/2lqFd
Somalia Mogadishu Bombenexplosion
Hoto: Reuters/F. Omar

Mazauna kusa da inda bam din ya tashi, sun ce karar fashewar ya yi tsanani irin wanda suka dade ba su ji irin karar ba a shekarun baya-bayannan. Wannan hari dai na zuwa ne kwanaki biyu da ganawar shugaban rundunar sojin Amirka a nahiyar Afirka, da shugaban kasar Somaliya.

To sai dai 'yan kasar na cike da fargabar ajiye aikin da misistan tsaron Somaliya ya yi, da babban kwamandan soji ba tare da bayyana hujjojin ajiye aikin ba.

 

Babu dai wadanda suka yi ikirarin kai harin kawo yanzu, amma kungiyar al-Shabaab na ci gaba da zama barazana a kasar Somaliya, inda ta sha daukar alhakin hari da ya sha ritsawa da jami'an tsaro da fararen hula, wannan ya sa a wannan shekara Amirka ta kaddamar da jiragen masu sarrafa kansu da nufin yakar kungiyar ta al-Shabaab.