1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar kamuwa da Omicron a Turai

Ahmed Salisu
January 11, 2022

Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO ta ce akwai yiwuwar fiye da rabin al'ummar da ke zaune a nahiyar Turai su kamu da cutar corona samfurin Omicron nan da makonni 6 zuwa 8 din da ke tafe.

https://p.dw.com/p/45O5C
Coronavirus - Virusvariante Omikron
Hoto: Andre M. Chang/ZUMA Press Wire/picture alliance

Reshen hukumar da ke nahiyar Turai ne ya sanar da hakan a wannan Talatar, yayin wani taron manema labarai da shugaban reshen Hans Kluge ya gudanar.

Mr. Kluge ya ce a makon farko na wannan sabuwar shekarar da muka shiga kimanin mutane miliyan bakwai ne suka kamu da cutar ta Corona, adadin da ya ce ya ninka wanda aka gani kafin shiga sabuwar shekarar.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kasashen Turai da ma na sauran sassan duniya ke fadi-tashi wajen al'umma sun karbi karin rigakafin corona din da nufin kare al'umma daga kamuwa da cutar nau'in Omicron, baya ga tsaurara matakan kariya da ake ci gaba da dauka.