Barnar da iska da ruwa suka haifar a Somaliya
November 13, 2013Iska mai karfin gaske ce ta fara kadawa a yankin Puntland na Somaliya kafin a fara shatatawa ruwa kamar da bakin kwarya. Kwararrun a fannin hasashen yanayi sun nunar da cewa yawan ruwan sama da aka yi a cikin kwana guda, ya kai adadin wanda ya kamata a samu a cikin watanni shida. Saboda haka ne ma maimakon gyara, ruwan ya hadassa barna ta rayuka da kuma dukiyoyi. Ko da shi ma Abdirzak Hassan na hukumar agajin gaggawa ta Somaliya sai da ya ce "sama da iyalai dubu 25 wannan bala'i ya shafa. An kuma tabbatar da mutuwar mutane akalla 143, yayin da mutane 150 suka bace."
Halin da ake ciki a Puntland bayan bala'in
A yanzu haka ma dai cututtuka irin su kwalera sun fara yaduwa a wannan yanki na Arewa maso gabashin Somaliya. Hakazalika dabbobi miliyan daya aka yi asararsu sakamakon ambaliya da ta biyo bayan iskar hade da ruwan sama. Da ma dai kiwo ne babbar kafa ta samun kudin shiga ga al'umar Puntland da ke cin kwarya-kwayar cin gashin kanta. Ga shin kuma talauci ya yi wa al'umar wannan yanki katutu. Tun ma kafin afkuwar wannan bala'in, 'yan yankin Putland na fama da karancin na sa wa a bakin salati. Saboda haka ne jami'in hukumar agajin gaggawa Abdirzak Hassan ya fara kira inda ya ce "Muna bukatan abinci cikin gaggawa, da kuma magunguna da kuma inda al'uma za su sa hakarkarinsu."
Ruwan da aka yi a Puntland ya lalata hanyoyi da dama, yayin da gadoji kuma suka kakkarye. Harkokin sadarwa kuma suka katse. Kungiyoyin agaji na cin karo da toshewar hanyoyi a kokarin da suke yi na kai kayan dauki da ake bukata a wannan yanki na Somaliya, a cewar Katharina Witkowski na Gamayyar kungiyoyin agaji ta World Vison. "Mun aika da manyan motoci hudu makare da kayayyakin agaji zuwa Puntland. Amma inda gizo ke saka shi ne hanyoyi suna toshe, saboda haka ba za su iya ci-gaba ba."
Rashin tsaro na dagula al'amura a Somaliya
Wani kalubalen da kungiyoyin agaji ke cin karo da shi a yankin Puntland na Somaliya shi ne na tsaro. Tun shekaru 20 da suka gabata yakin basasa ya daidaita kasar tare da mayar da ita tungar 'yan fashin teku da kuma masu gaggwarmaya da bindigogi. Yanki ma da bala'in na kadawar iska hade da ruwan sama ya shafa ba a shiganshi ta sauki. Hanya daya tilo da ake zuwa yankin na Puntland na hannun masu kaifin kishin Islama na al-Shabaab da sauran kungiyoyin da ke gaggwarmaya da makamai.
Puntland dai na daga cikin daidaikun yankunan Somaliya da suke da tsayayyun gwamnati. Ko da shi ke ba burin yankin ba ne ya raba gari da gwamnati tsakiya ba, amma kuma Puntland ya ayyana kanta a matsayin mai kwarya-kwarya 'yancin tafiyar da al'amuranta ba tare da tsoma bankin gwamnatin tsakiya ba. A shekarun baya-bayannan dai ta tashi tsaye tare da taimakon hukumomin agaji wajen yakar ayyukan ta'addanci da kuma fashin teku. Katharina Witkowski ta World Vision ta yi karin haske.
"A yanzu haka a yankunan arewanci, al'amuran tsaro sun fara inganta. Mun yi nasarar fita a shekarar da ta gabata daga matsayi na dokar ta baci, i zuwa . Sannan yanzu babin ayyukan ci-gaba. Mun ma kaddamar da ayyukan raya kasa."
Gwamnatin Puntland da kanta ta yi kira da a agaza mata. Amma kuma taimakon da ya isa wannan yankin na Somaliya bai taka kara ya karya ba.
Mawallafiya: Hilke Fischer/ Mouhamadou Awal
Edita: Pinado Abdu-Waba