Barnar Tsunami A Somaliya
January 7, 2005Ita dai kasar Somaliya yau kimanin shekaru 14 ke nan take fama da yamutsi tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Siad Barre a 1991, kuma a hakika ma ana iya cewar bata da wata tsayayyar gwamnati yanzu haka. Babu tabbatattun alkaluma da aka bayar dangane da yawan mutanen da suka jirkata a gabar tekun kasar Somaliyar. A dai ranar da tsautsayin ya wakana akasarin masuntan kasar na bakin aikinsu a cikin kwale-kwale, kuma MDD ta kiyasce yawan mutanen da suka yi asarar rayukansu ya kai dari biyu zuwa dari uku, a baya ga wasu dubu 17 zuwa dubu 54 da suka tagayyara suke kuma bukatar taimako na gaggawa. An saurara daga bakin Laura Mello, mai magana da yawun kungiyar taimakon abinci ta MDD a Nairobi tana mai bayanin cewar ba wanda zai iya tantance irin barnar da mahaukaciyar igiyar ruwa ta tsunami tayi wa kasar Somaliya. Tuni kungiyar ta tura wata tawagarta domin taimako da kuma bitar barnar da masifar tayi wa kasar. Bayanai da aka tara zuwa yanzu sun nuna cewar sama da mutane dubu 30 ne bala’in ya shafa. Wadannan mutanen su yi asarar gidaje da dukkan kadarorin da suke mallaka, kuma ba su da ikon ci da kansu da kansu. Lamarin ya fi tsamari a lardin Putland, mai kwaryakwaryar ikon cin gashin kansa a arewa-maso-gabacin Somaliya. A tsuburin Hafun, wanda kusan mahaukaciyar igiyar ruwan ta bannatar da shi kwata-kwata, mutane sun haye kan wani tudu ne dake yankin domin kubutar da rayukansu. Masuntan da suka fita kamun kifi a wannan rana, kusan babu daya daga cikinsu da ya dawo gida. Igiyar ruwan tayi kaca-kaca da dukkan hanyoyin sadarwa a yankin, ta yadda matocin dake dauke da kayan taimako ke fama da wahala wajen kai gudummawa. Laura Mello ta ce kungiyar taimakon abincin ta MDD bata yi wata-wata ba wajen tura manyan motoci dauke da kayan masarufi zuwa yankin Hafun, amma ba su samu ikon kutsawa wannan yanki ba. Wannan bala’in dai ya zo wa kasar Somaliya a daidai lokacin da ta fara samun bunkasar ayyukanta na kamun kifi. Da yawa daga makiyaya na kasar sun canza sana’a zuwa sana’ar kamun kifi, wacce a yanzun ta zame musu kayar kifi a wuya. A yau juma’a kungiyar taimakon abinci ta MDD ta fara jigilar abinci da magunguna da barguna ta jiragen ruwa daga Mombasan Kenya zuwa arewacin Somaliya. Sabuwar gwamnatin hijira da aka nada ba ta da tasiri saboda har yau haulakan yaki ne ke da fada a ji a kasar. Duka-duka abin da kungiyar taimakon abincin ta MDD zata iya yi dai shi ne gabatar da kira ga sauran kafofi na kasa da kasa da ka da su yi ko oho da makomar Afurka a rubibinsu na ba da taimako ga kasashen Asiya. Laura Mello ta ce kungiyar na bukatar dala miliyan biyu da dubu dari takwas a cikin gaggawa domin taimaka wa mutanen da masifar ta tsunami ta rutsa da su a kasar Somaliya.