Bayern za ta kara da PSG a wasan karshe
August 20, 2020Kungiyar Bayern Munich ta nan Jamus ta samu tikitin zuwa wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai bayan da a daren jiya Laraba ta yi nasarar doke kungiyar Lyon ta kasar Faransa da ci uku da nema a wasa na biyu na kusa da na karshe da suka fafata a birnin Lisbon na Potugal.
A ranar Lahadi mai zuwa ce idan Allah ya kai mu Kungiyar ta bayern Munich za ta fafata a wasan karshe da kungiyar PSG ta kasar Faransa wacce ta doke Leipzig ta Jamus da ci uku da nema a wasan kusa da na karshe na farko a ranar Talatar da ta gabata.
Sau biyar dai ne a baya da kungiyar ta Bayern Munich ke daukar kofin zakarun Turai, a yayin da daga nata bangare Kungiyar PSG wannan shi ne karo na farko shekaru 50 bayan kafa kungiyar da za ta buga wasan karshen na neman cin wannan kofin zakarun Turan.