Bayyanar cutar dan sakarau a Burkina Faso
January 23, 2016Talla
Gidajen asibitoci dai sun sanar da bullar wasu cutuka da ke da saurin yaduwa a kasar ta Burkina Faso tun daga ranaikun 4 zuwa 10 ga wannan wata na Janairu kuma cikinsu an samu mutane akalla 63 da suka kamu da cutar dan sankarau, inda biyar daga cikinsu suka rasu a cewar sanarwar.
Hukumomin lafiyar kasar ta Burkina Faso dai sun sanar cewa, yawan wadanda suka kamu da cutar ya karu da mutum 29 idan aka kwatanta shi da na shekarar da ta gabata a daidai wannan lokaci. A shekarar da ta gabata dai kasashen irin su Nijar da Najeriya sun fuskanci babbar matsala dangane da wannan cuta ta dan sankarau.