1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Bikin tunawa da zuwan addinin Kirista a Jamhuriyar Nijar

December 10, 2024

An yi bikin cikashekara 100 da Turawa 'yan Mission su kawo addinin Kirista a garin Maza Tsaye na Maradi da ke Jamhuriyar Nijar da ke zama wurare na farko da aka fadada addinin a kasar.

https://p.dw.com/p/4nyHu
Mabiya addinin Kirista
Mabiya addinin KiristaHoto: Luis Tato/AFP

Albarkacin haka al'umar Kirista a kasar da Turawa na kungiyar SIM Nijar sun shirya kasaitacen bikin a garin Maza Tsaye da ke jahar Maradi. A ckin harabar Eklisiyar garin Maza Tsaye ne da ke cikin jihar Maradi cikin ikon gundumar Gidan Rumji da'ira Tibiri aka gudanar da shagulgula na bikin cika shekara 100 da shigowar adinin Kirista ta hanyar Turawa mabiya na kungiyar SIM.

Karin Bayani: Shirin bikin Kirsimeti a Najeriya da Nijar

Alamar Gicciyewa
Alamar GicciyewaHoto: Hasenonkel/YAY Images/IMAGO

An dai yi bikin karkashin jagorancin shugabanin adinin Kirista na kungiyar SIM ta kasa da na jahohi da saura baki mabiya daga sassa daban-daban inda aka gudanar da shagulgula da suka hada da jawabai, tarihi, addu'o'i, kade-kade da wake-waken yabo Yesu Almasihu. Shi kuma Raverand Hashimu Usman shugaban kungiyar Ameen kungiyar hadin kan kungiyoyin addinin Kirista na jihar Maradi ya ce wannan biki ne da ba za a taba mantawa da shi ba a kasar. An samu halartar Turawa mabiya maza da mata masu jin harshen Hausa da suka halarci bikin daga sassan kasar kamar Zinder, Tahoua, Yamai, Dosso da kuma Maradi mai masaukin baki 

A karshen bikin an karrama shugaban kungiyar SIM na kasa Jonathan Moor kan kokari da gwagwarmaya da ya yi cikin wannan aiki na bushara. Shagulgulan dai za su ci gaba tsawon mako guda inda za a gabatar da laccoci da wa'azi na kara karfama mabiya a cikin Eklisiyoyi daban-daban.