Matsin lamba ga gwamnati don binciken kisan fararen hula
March 11, 2020Talla
Da yake gabatar da bukatar a babban birnin Ouagadougou, mataimakin shugaban jam'iyyar UPC mai adawa a kasar Amadou Diemdioda Dicko ya ce 'yan adawar sun kadu da jin kisan na fararen hula har mutum 43, kana kuma ba za su yi wata wata ba suna bukata ga gawamnatin kasar da ta kaddamar da bincike kan musabbabin kisan.
A ranar Lahadin da tagabata ne dai wasu dauke da makamai da kawo yanzu ba a kai ga tantancewa ba suka kaddamar da harin kan mai uwa da wabi a wasu garuruwan Fulani da ke arewacin kasar mai iyaka da Mali, tare da kisan mutanen da ba su san hawa ba su san sauka ba su akalla mutum 43, wanda har ta kai ga gwamnatin kasar ware zaman makoki na kwanaki biyu.