1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Likitan da ya gano Coronavirus ya mutu

Abdul-raheem Hassan
February 8, 2020

Gwamnatin Chaina ta sha alwashin binciken bin diddigi kan mutuwar likitan da ya fara gano bullar annobar cutar Coronavirus a Wuhan.

https://p.dw.com/p/3XS8q
Coronavirus China Suining Produktion Schutzmasken
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/Chinatopix

Mutuwar kwararren likitan mai suna Li Wenliang mai shekaru 34 da ya shahara a binciken cutattukan yanar ido, ya sa gwamnatin Chaina fara tunanin hakikan abinda ya kashe likitan ko yana da alaka da cutar Coronavirus.

Hukumomin Chaina sun tsare likitian bayan sanar da bullar cutar a watan Disamban 2019 saboda nuna shakku kan cutar, kamin daga baya aka tabbatar da barkewar cutar a karshen shekarar 2019. Da farko ana zargin wata tsohuwar cutar numfashi ce ta dawo wacce ta kashe daruruwan mutane a shekarun 2002 zuwa 2003.

Yayin da gwamnati ta nada kwamitin bincike domin gano hakikanin sanadiyar mutuwar likitan, al'umma da dama a Chaina na yada mutuwar likitan a shafukan sada zumunta a matsayin wani gwarzon namiji da ya fara ankarar da da mutane kan cutar. Yanzu haaka dai an tabbatar cutar ta kashe mutane 722 ta kuma kama akalla mutane 34,546 a sassa daban-daban na duniya.