1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta raba gari da kungiyar EU

Abdullahi Tanko Bala AAI
January 31, 2020

Birtaniya ta kafa tarihi inda ta kasance kasa ta farko da ta fice daga kungiyar tarayyar Turai. A baya Birtaniyar ta kasance mai karfin fada a ji wajen tsara manufofi da kuma inda aka dosa a kawancen EU.

https://p.dw.com/p/3X61X
Tutocin kungiyar taraiyar Turai da ta Birtaniya a yayin kokarin raba gari
Tutocin kungiyar taraiyar Turai da ta Birtaniya a yayin kokarin raba gariHoto: Getty Images/AFP/T. Akmen

Birtaniya ta kasance kasa ta farko da ta ware daga cikin kasashe 28 mambobin kungiyar EU tun shekara ta 1973. Firaminista Boris Johnson ya jima da goyon bayan aniyar kasar ta ficewa daga kungiyar tun a shekara ta 2016 lokacin da mahukuntan kasar suka kaddamar da kuri'ar ficewar. Al'amarin dai tun a baya ya haifar da rarrabuwar kai da mabanbantan ra'ayoyi, inda a yanzu haka ma Firaminista Johnson din ya daukar wa al'ummar kasar alwashin ingantacciyar makoma.

Gwamnatin Birtaniya ta umarci takaita bukubuwan farin cikin ficewar kasar daga EU domin karrama da dama daga cikin al'ummar kasar wadanda suke kyamar wannan mataki da kuma wadanda suke fargabar makomar kasar ta Birtaniya a nan gaba.

Gungun masu goyon bayan barin kungiyar EU
Gungun masu goyon bayan barin kungiyar EUHoto: Getty Images/AFP/T. Akmen

A shekarun da suka gabata kawance tsakanin Kungiyar tarayyar Turai da Birtaniya ba ta kasance da sauki ba. Lamarin da ya baiyana a manufofin harkokin waje da kuma na tsaro. London kan zama garkuwa idan aka yi maganar hadin kai ta fannin soji alal misali. A daya bangaren kuma Birtaniya babbar jigo ce wajen manufofin harkokin waje. Reinhard Bütihofer dan majalisar dokokin turai na jam'iyar green na mai ra'ayin cewa kungiyar tarayyar Turai za ta sami nakasu bayan ficewar Birtaniya.

"Ya ce Birtaniya kasa ce wadda ta kware a fagen diflomasiyya. Birtaniya na da kujerar dundundun a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, haka nan Birtaniya ta fi dukkanin kasashen turai idan aka yi magana ta karfin soji".

Bütihofer ya bada shawarar ci gaba da dangantaka ta kut da kut da Birtaniya bayan ta fice ba tare da nuna fifiko ba. A baya bayan nan ma shugaban kula da manufofin harkokin waje na kungiyar EU Josep Borrel a wata hira da aka yi da shi ya baiyana cewa dangantaka ta fannin manufofin tsaro ta na da muhimmanci ga bangarorin. Ya ce suna da ra'ayi daya, a fagen siyasar duniya. Akwai kuma batutuwa da dama da ya kamata su hada hannu su yi aiki tare. Kama daga sanya takunkumi zuwa wasu batutuwa masu muhimmanci da fannin hukumomin leken asiri da yaki da labarun karya da kuma yaki da muggan laifuka ta yanar gizo.

A yanzu dai babu tabbas kan yadda karfin dangantakar za ta kasance tsakanin Kungiyar tarayyar Turai da Birtaniya. A yarjejeniyar rabuwar da bangarorin biyu suka rattaba wa hannu, an zayyana kudiri ne kawai na niyya, kalamai dai masu dadi cewa Birtaniya na iya shiga cikin wasu muhimman ayyukan soji ko ma ci gaba da yin aiki a rundunar kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Turai. Dan majalisar dokokin Turai David Mc Allister daga jam'iyyar CDU ya goyi bayan wannan matsayi.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson a tsakiya
Firaministan Birtaniya Boris Johnson a tsakiyaHoto: picture-alliance/empics/D. Lawson

"Damar ta nan. Sai dai kuma a bayane yake duk kasar da ta fice daga kungiyar tarayyar Turai, ba za ta taba jagorantar kasashen a irin wadan nan ayyukan kiyaye zaman lafiya ba. Saboda haka ba zai yiwu Birtaniya ta sami wani jagoranci ba."

A sakamakon ficewar Birtaniyar daga kungiyar tarayyar Turai, dokokin da za a yi amfani da su wajen mu'amala da ita sun banbanta da dokokin da za a yi amfani da su wajen  mu'amala da sauran kasashe da ke cikin EU a cewar Fabian Zuleeg na cibiyar nazarin manufofin tarayyar Turai.

"Ya ce tabbas kungiyar tarayyar Turai ba za ta kyale Birtaniya ta shiga hukumomi da za su zartar da hukunci ba, wannan na nufin cewa dole ne Birtaniya ta bi dokokin tarayyar Turai ba tare da tana da wata ta cewa ba."

Tambayar ita ce shin wane shiri Birtaniya ta yi? a hannu daya kuma wane sassauci kungiyar tarayyar Turai za ta iya yi mata? a don haka akwai yiwuwar tattaunawar ta yi tsauri. Hatta a kan kawance a fannin hukumomin leken asiri da na 'yan sanda kamar yadda Fabian Zuleeg ya ke cewa.

Sai dai kuma kwarraru sun yi hasashen cewa manufofin harkokin waje da na tsaro za su zama a karshen jadawalin batutuwan tattaunawa tsakanin Kungiyar tarayyar Turai da Birtaniya idan aka yi la'akari da makomar dangantaka a tsakaninsu ta fuskar tattalin arziki.
.