Bisa Williams ta Amirka ta kai ziyara Burkina
November 8, 2014Talla
Ƙaramar Sakatariyar harkokin wajen Amirka da ke kula da nahiyar Afirka Bisa Williams ta kai ziyarar bazata birnin Ouagadougou na Burkina Faso, kwanaki ƙalilan bayan saukar Blaise Compaore daga ƙaragar mulki ba girma ba arziki.Babbar jami'ar dipolamisiyar ta gana da shugaban mulkin sojen ƙasar Lt Co Isaac Zida
Babu dai wanda ya san adadin kwankin da jami'ar za ta shafe a Burkina Faso da kuma abin da agendarta ta kunsa. Amma dai Amirka na sahun gaba wajen matsawa sojojin lamba domin su mayar da mulki a hannun farar hula bayan da guguwar mulki ta yi awon gaba da gwamnatin Blaise Compaore.