1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Blaise Compaore na fuskantar shari'a

Gazali Abdou Tasawa
April 27, 2017

Wata kotu a birnin Ouagadougou na Burkina Faso ta soma yi wa tsohon shugaban kasar Blaise Compaore shari'a a bayan idon sa tare da wasu tsofin manbobin tsohuwar gwamnatin.

https://p.dw.com/p/2c0u6
Blaise Compaore Präsident Burkina Faso
Hoto: REUTERS

Ministoci 34 na majalissar minitocin tsohuwar gwamnatin kasar ta Burkina Faso za su bayyana a gaban kotun kolin kasar da ke a birnin Ouagadougou domin kare kan su daga zargin da ake yi musu na amfani da gwamnatin ta su, ta yi da karfin bindiga wajen murkushe masu zanga-zanga. A boren da al'ummar kasar ta yi wa gwamnati a shekara ta 2014 da ya kai ga korar shugaba Blaise Compaore da gwamnatin sa daga mulki. Sai dai tsohon shugaban kasar Blaise Compaore ba zai halarci zaman shari'ar ba kasancewa yanzu haka yana zaman gudun hijira a kasar Cote d'Ivoire. Blaise Compaore dai ya share shekaru 27 kan karagar mulkin kasar ta Burkina Faso kafin al'ummar kasar ta yi masa korar kare a karkashin wani bore a shekara ta 2014 wanda ya barke a loakcin da shugaban ya yi yinkurin yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin samun damar ci gaba da yin mulki a karshen wa'adin sa.