Boris Johnson ya sha kaye a majalisar dokoki
September 10, 2019Gabanin jefa kuri'ar a yammacin jiya Boris Johnson ya bukaci da a gudanar da zaben maye gurbi na 'yan majalisun dokoki a ranar 15 ga watan Oktoba mai zuwa, domin samun rinjaye a majalisar da kan iya bashi wata dama ta fitar da kasar daga EU ko babu yarjejeniya da kungiyar.
Wannan dai shi ne karo na biyu a kasa da kwanaki biyar da majalisar dokokin Birtaniya ta yi fatali da bukatar Firaminista Johnson da ke fafutikar ganin Birtaniyar ta fita daga EU ko ta halin kaka, batun da 'yan majalisun dokokin kasar masu rinjaye suka yi fatali da shi.
Masu sharhi na bayyana cewa dubara ta rage ga firaministan a yanzu duba yadda al'amurra suka kara rincabewa kan batun sake dage ranar ficewar Birtaniya da EU, sai dai a wata ziyarar aiki da ya kai a birnin Dublin na kasar Ireland, Boris Johnson ya bayyana fatan fitar kasar da wata yarjejeniya, to amma sai dai bangarorin biyu ba su kai ga cimma wata matsaya ba kan wasu muhimman batutuwa.