An aminta da yarjejeniyar da Eu ta cimma da Birtaniya
December 28, 2020Talla
Jakadodin kasashe memebobin Kungiyar Tarayyar Turai, sun sahalewa kungiyar EU soma aiki da yarjejeniyar kasuwancin nan maras shinge da ta cimma da Biratniya a farkon watan sabuwar shekara.
Wannan matakin na a matsayin share fagen soma amfani da daftarin yarjejeniyar ce da aka cimma a makon jiya, a gabanin na shugabanni da gwamnatocin kasashen, da ake sa ran su ba da ta su amincewar a gaba.
Kuma ana sa ran ranar Laraba, majalisar dokokin Biratniya ta kada kuri'ar na'am da sabon daftarin yarjejeniyar kasuwancin, kwanaki kalilan a gabanin ficewar Biratniya da kungiyar.