1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar kawo karshen cin zarafin 'yan Jarida a duniya

November 2, 2017

Yayin da ake bikin tunawa da ranar kawo karshen cin zarafin 'yan jarida, kungiyar 'yan jaridu ta kasa a tarayyar Najeriya NUJ ta ce har yanzu ‘yan jaridar na fuskantar cin zarafi a cikin kasar.

https://p.dw.com/p/2mwC7
Großbritannien Berichterstattung Terroranschläge von Barcelona
Hoto: Getty Images/AFP/R. Bodman

Babban rikicin dai na zaman gwagwarmaya ta nuna isa a tsakanin masu takama da karfin bindiga, da kuma ‘yan uwansu da ke takama da karfin biro a ko’ina cikin tarrayar Najeriya. An dai doke da dama kuma farfasa kayan aiki na kafafen labarai daban daban cikin tarrayar Najeriyar wanda ke nuna alamun karuwar tozartarwa ga ‘yan jaridar.

Tansania Polizei attackiert einen Journalisten in Dar es Salaam
Jami'an tsaro na cin zarafin wani dan Jarida a Dar es Salam na kasar TanzaniyaHoto: Article19-East Africa

Wannan yasa kungiyar yan jaridar Najeriyar koka wa da nufin neman  hanyar kawo karshen matsalar dake karuwa. A makon da ya gabata ma sai da wani karamin hafsan soja cin zarafin wani mai daukar hoto na kamfanin Media Trust da ke kokarin aikinsa wajen wani hatsarin mota a Abuja.

Tashar Deutsche Welle ma bata tsira ba a hannun jami’an tsaro inda suka lalata kayan aikin wakilinta a tsakiyar wannan shekarar ta 2017 a kaduna.

Nigeria Presse - Der Fall Dasuki und die Ermittlungen des EFCC
Wasu ma'abota karanta Jarida a Abuja NajeriyaHoto: DW/A. Kriesch

Sau 12 dai ‘yan jaridar suna fuskantar barazana a cikin watanni 11 da suka shude a Najeriya a  cewar Shu’aibu Leman sakataren kungiyar ‘yan jarida ta kasar.

Kokarin neman diya ko kuma neman hanyar taka birki ga karuwar cin zarafin dai na nuna alamar barazanar da makoma mara tabbas da aikin jarida ke fuskanta a yanzu.

A cewar Auwal Mua’zu editan wata jaridar mai zaman kanta ta Daily Stream, bullo da sabbabin dokokin hukunta masu cin zarafi ‘yan jarida ya zama wajibi domin ceto aikin.