An soma gudanar da bukukuwan Kirismeti
December 24, 2024A bana dai, bikin Kirsimeti bai shiga zuciyar Nadège Sebujangwe ba, wata yarinya 'yar shekara 13 da ke gudun hijira, wacce babban abin da ke damunta shi ne 'yunwa da ke barazana ga rayuwarta a sansanin Don Bosco da ke gabashin Kwango.
"Tun da mu ka guji yaki, mun sha wahala sosai. Mu kan kwana ba mu sa komai a bakin salati ba. A gaskiya, ba na tuna bikin Kirsimeti ko kadan. Idan da muna gida, da iyayenmu sun saya mana sababbin tufafi kuma sun shirya liyafar abinci. Idan masu hannu da shuni suna ji mu, su taimake mu domin mu sami abin da za mu ci, da samun tufafin da za mu saka."Damuwar wannan matashiya ta yi daidai da na iyayen yara da yakin ya raba da muhallansu. Daidai da Amani Vunabandi, mahaifin 'ya'ya bakwai yana fuskantar talauci a halin yanzu, saboda haka ne yake da burin komawa kauyensa na Rugari da zarar an samu zaman lafiya domin kirsimeti badi ya fi na bana kyau.
"Lokacin da muke gida a Rugari, muna hada gwiwa a kungiyance,ta hanyar tara kudi. A kowace karshen shekara, wannan ya ba mu damar sayan nama da tufafi don 'ya'yanmu su gudanar da bikin kirsimeti cikin annushuwa. Amma a wannan sansanin 'yan gudun hijira, ba mu da wata hanya ta samun kudi. Ko samun abinci ma yana da wahala. Muna rokon gwamnati da ta dawo mana da zaman lafiya domin mu koma garuruwanmu."
A kokarin sanya murmushi a fuskokin 'yan gudun hijirar, musamman kananan yara, kungiyoyin matasa da dama a birnin Goma suna gudanar da gangamin tattara kayan agaji. Moïse Muhindo, mamba na kungiyar Sant'Egidio, ya bayyana cewa taimakon da aka tattara na da yawa kuma sun bambanta. "Mun ga an manta da yaran da ke sansanin 'yan gudun hijira, da kuma iyayensu. A namu bangaren, mun yanke shawarar wayar da kan jama'a domin tunatar da su cewa akwai 'yan uwanmu mata da abokanmu da ke zaune a wadannan sansanonin. Wannan ne ya sa kuke ganin muna bi gida-gida muna karbar tufafi, kudi da abinci, domin su ma wadannan mutanen da suka rasa matsugunansu su samu wani abin da za su gudanar da bukukuwan Kirsimeti." Bukukuwan na Kirsimeti na gudana ne cikin yanayi na tashin hankali a lardin Kivu ta Arewa da ke gabashin Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango, inda ake ci gaba da gwabza fada tsakanin 'yan tawayen M23 da sojojin gwamnatin Kwango.