Bunƙasar kasuwanci a Somaliya
December 9, 2011A wannan makon ma dai taron majalisar duniya akan makomar yanayi a Durban ta Afirka ta Kudu shi ne ya fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus, inda jaridar Suüddeutsche Zeitung ta ce sabani tsakanin kasashe masu ci gaban masana'antu da masu matsakaicin ci gaban masana'antu na barazanar sanya murna ta koma ciki game da fatan da aka na cimma wata sabuwar yarjejeniyar kare makomar yanayi a zauren taron Durban. Domin kuwa har yau mahalarta taron sun kasa cimma daidaituwa a game da tallafin da ya kamata a ba wa ƙasashe 'yan rabbana ka wadata mu da matakan da suka cancanta don kare makomar dazuzzukan kurmi da kuma ƙayyade yawan gubar carbondioxid da ƙasashe masu ci gaban masana'antu ke fitarwa zuwa sararin samaniya, wadda ita ce ainihin ummalaba'isin ɗimamar yanayin da ake fama da ita.
A nata ɓangaren jaridar Neues Deutschland ba da misali tayi da ƙasar Habasha, wadda al'umarta ke fama da ƙarancin abinci sakamakon canje-canjen yanayin da ake samu, inda ƙasar ke fama da ruwan sama ba ƙaƙƙautawa, lamarin dake barazana ga amfanin noma a Habashar.
A can ƙasar Kongo har yau ana ci gaba da fama da mawuyacin hali na zaman ɗarɗar kuma Angola tayi barazanar yin katsalandan na soja kamar yadda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rawaito. Jaridar ta ce:
Ƙasar Afirka ta Kudu, wadda ita ce ta dauki nauyin zaɓen ƙasar Kongo da aka gudanar ta fito fili tayi Allah waddai da barazanar da ƙasar Angola tayi game da katsalandan soja a ƙasar Kongo in har al'amura sun ci gaba da taɓarɓarewa. Bisa ga ra'ayin gwamnatin Afirka ta Kudu irin wannan katsalandan na soja tilas ne ya samu amincewa daga kungiyar raya kudancin Afirka ta SADC, wadda dukkan ƙasashen Angola da Kongo da ita kanta Afirka ta Kudun ke ƙarkashin inuwarta. Kuma Afirka ta Kudun ta ce ba zata taba amincewa da irin wannan mataki ba.
A wani ci gaban kuma, kamar yadda jaridar Süddeutsche Zeitung ta rawaito, a ƙasar Somaliya, a yayinda a ɓangare guda ake fama da matsalar yunwa, amma kuma a ɗaya ɓangaren tattalin arziƙin ƙasar sai bunƙasa yake yi, inda tsarin jari-hujja ya kankama. Jaridar ta ce a halin yanzu haka duk mai iko, muddin yana da sulalla a hannunsa zai iya sayen dukkan abin da yake buƙata a ƙasar Somaliya. Dukkan kafofin da a da suke hannun gwamnati a yanzu sun koma hannun ɗaiɗaikun mutane masu zaman kansu, kama dai daga makarantu zuwa ga kiwon lafiya da kuma tsarin bankuna. Abu ɗaya da masu hannu da shuni a ƙasar ke buƙata shi ne 'yan banga dake tsaron lafiyarsu. To sai dai kuma a inda take ƙasa tana dabo shi ne miliyoyin mutane 'yan rabbana ka wadatamu, waɗanda da ƙyar ne suke samun abin sakawa bakin salati a ƙasar da yaƙin basasa yayi kaca-kaca da ita kuma mawadata ne kawai ke more wannan mawuyacin hali da ƙasar ta samu kanta a ciki tun shekaru gommai da suka wuce....
Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal
Edita: umaru Aliyu