Dokar hana yada labarai kan tsaro a Burkina
June 22, 2019Dokar ta tanadi hukunta duk mutumin da ya wallafa wasu hotuna ko bidiyo na hare-haren da sojojin kasar suke fuskanta daga 'yan ta'adda, ko na mutanen da harin ta'addanci ya ritsa da su, ko kuma duk wasu hotuna ko bidiyo da ka iya taimakawa wajen sanyaya gwiwar sojojin kasar da ke yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda.
Gwamnatin Burkina Faso ta ce burin da take son cimma a cikin wannan doka shi ne sa ido kan labaran da ake yadawa domin kauce yi wa kungiyoyin 'yan ta'adda farfaganda.
Sai dai 'yan majalisar dokoki na bangaren adawa sun fice daga zauren majalisar kafin soma muhawarar, suna masu zargin cewa gwamnatin ba ta yi wa jama'a cikakken bayani kan dokar ba. Suma dai kungiyoyin 'yan jarida na kasar ta Burkina Faso sun soki lamirin dokar wacce suka bayyana a matsayin tauyin 'yancin aikin jarida a kasar.