Harin ta'addanci ya hakllaka mutane a Burkina Faso
December 25, 2019Talla
Fararan hula akalla 35 ne ciki galibi mata ne suka hallaka sakamakon wani harin ta'addancin da ake kyautata zaton mayakin jahadi ne suka kai shi a yankin Arbinda da ke arewacin kasar Burkina Faso, adadin da ke zama irinsa mafi muni da ya auku kan fararen hula a kasar. Tuni kasar ta ayyana zaman makoki na kwanaki biyo bayan harin na ta'addancin, sai dai ko bayan ga fararan hular da suka hallaka wasu sojojin kasar bakwai sun gamu da ajalinsu a cikin harin.