Burkina Faso: An hana yawon dare da babura
September 20, 2018Talla
Gwamnan yankin Gabashin kasar Kanal Ousmane Traore ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Dokar za ta yi aiki daga karfe bakwai na yamma zuwa karfe biyar na safe. Sai dai kuma gwamnan ya ce matakin ya tanadi tsaurara bincike kan sauran motocin fasinja da na daukar kaya wadanda dokar ba ta haramta masu ci gaba da zirga-zirgar ba.
Kazalika matakin ya tanadi ci gaba da rufe wuraren hako ma'adanai a gargajiyance wadanda ke aiki da ababe masu fashewa kirar gargajiya wadanda sau tari aka yi amfani da su wajen kai hari kan jami'an tsaro a watanni baya bayan nan a kasar.