Burkina Faso da Mali na son kawar da ta'addanci
January 18, 2016Kungiyar dai ta bayyana sunayen Battar al-Ansari da Abu Muhammad al-Buqali al-Ansari da kuma Ahmed al-Fulani al-Ansari a matsayin wanda suka afkawa Otal din na Splendid ranar Juma'ar da ta gabata inda suka yi sanadin hallakar mutane 28 wanda 'yan kasashen waje ne da suka sauka a Otal din. A wani sako da ta fidda a shafin Intanet, kungiyar ta sanya hotunan mayakan nata wanda dukanninsu matasa ne sanye da kayan soji, dauke da manyan bindigogi, kana ta ce mayakan sun kai hari Otal din ne kasancewarsa wata cibiya a yammacin Afirka da ake amfani da ita wajen cin amana ta kasashen duniya.
Wannan ne ma ya sanya Mali da ita kanta kasar ta Burkina Faso da wannan hari ya shafa yanke shawarar yin aiki tare da nufin ganin hare-hare na ta'addanci da ke kokarin gagarar kundila a yammacin Afirka ya zama tarihi. Sai dai masu sharhi kan lamuran siyasa da harkoki na tsaro irinsu Imad Mesdoua na ganin wannan ba karamin aiki ba ne ga kasashen duba da wasu kalubale da suke fuskanta wanda suka hada da rashin kwarewa da kuma karancin kudi.
Wani lamari har wa yau da ake kallo a matsayin abin da zai yin tarnaki ga yunkurin kasashen biyu shi ne yiwuwar rashin samun tallafi daga kasashen da wannan matsala ta sha da ma irin lokacin da za a dauka kafin a ace an kai ga cimma wadannan 'yan ta'adda. To sai dai yayin da masharhanta ke wannan tsokaci, firaministan Burkina Faso Paul Kaba Thieba ya ce ba za a ce su na da rashin kwarewar da za su iya tinkarar 'yan ta'adda ba matsala guda kawai da suke da ita ba ta wuce ce ta irin salon da mayakan ke amfani da shi wajen kaddamar da hare-harensu.
Yanzu haka dai hukumomi a Burkina Faso da Mali ma sauran kasashen da ke makota da wadannan kasashe sun tashi tsaye wajen ganin sun girka matakan tsaro domin hana duk wata kafa da za ta taimaka wajen kai hari kasashensu musamman ma inda baki 'yan kasashen yammacin duniya suka fi zuwa.