Wasu matasa sun kai hari a ofishin 'yan sanda a Burkina Faso
January 19, 2019Talla
Ma'aikatar tsaron kasar ta bayyana cewar tawagar wasu samari da yawansu ya kai 100 sun afka ofishin 'yan sanda na birnin Orodara da ke yammacin kasar da niyar daukar fansar wani matashi da jami'an tsaron suka harbe a ranar Juma'ar da ta gabata. Sakamakon binciken gaggawar da ma'aikatar tsaron kasar ta gudanar ya tabbatar da mutuwar biyar daga cikin matasan yayin da takwas suke cikin mawuyacin hali sakamakon muggan raunuka.