1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Burkina Faso sun kashe 'yan ta'adda 47

Abdourahamane Hassane
May 20, 2020

Rundunar sojojin Burkina Faso ta ce ta yi nasarar kashe yan ta'adda 47 a wani sumame da ta kai a Waribere da ke a yankin  arewa maso yammaci na kasar, sai dai ta ce an kashe musu sojoji biyu.

https://p.dw.com/p/3cYTA
Afrika 2017 | Burkina Faso | Soldaten im Einsatz
Hoto: Imago Images/ZUMA Press/B. Slessman

Shugaban askarawa na Burkina Faso Janar Moise Moningou ya ce harin na bazatan da suka kai a lardin Kossi da ke kan iyaka da Mali ya ba su damar lalata makaman 'yan ta'addar tare da kwace wasu. Tun daga shekara ta 2015 hare-haren 'yan ta'addar a Burkina Faso sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 850 yayin da suka tilasta wa wasu kusan dubu 840 yin kaura.