Burkina Faso: Kawar da yunkurin juyin mulki
October 21, 2016
Cikin wata sanarwa ce dai ministan cikin gidan kasar Simon Compaoré, ya ce wani gungu ne na sojoji fiye da 30 suka tsara kai hari a ranar takwas ga wannan wata na Octoba a wasu mahimman wurare ciki kuwa har da fadar Kossyam ta shugaban kasar ta Burkina Faso da zimmar kwace mulki.
Ministan ya ce a tonon asirin da wasu 'yan uwansu sojoji na tsofuwar rundunar RSP suka yi, sun ce Ajudan Coulibali Gaston, tare da goyon bayan Sajen Zerbo Khalifa, da soja Yelemu Issaka su ne suka kasance jagororin kulla wannan makalkashiya.
Ministan cikin gidan na Burkina Faso, ya ce masu yunkurin juyin mulkin sun tsara za su fitar da abokansu na tsofuwar rundunar ta RSP da ake tsare da su a gidajen kurkuku tun bayan juyin mulkin da bai yi nasara ba na lokacin mulkin rikon kwarya, sannan ya ce gabaki dayan su sojoji 32 da fararan hulla 10 an mikasu ga hannun shari'a.