Burkina Faso: Rikici ya hallaka mutane 46
January 4, 2019Talla
Rikicin dai ya wakana ne a kauyen Yirgu da ke gundumar Barsalogo inda mutane 13 suka rasu, daga bisani mazauna Yirgu din wanda 'yan kabilar Mossi ne suka afkawa wasu Fulani makiyaya wanda suka zarga da hadin baki da maharan da suka far musu, batun da ya sanya yawan wanda suka rasu din ya karu.
Burkina Faso dai na daga cikin kasashen Afirka, da ke fuskantar hare-haren na masu tsaurin kishin addini da kuma fadace-fadace na kabilanci, wanda a wasu lokutan hukumomi a kasar suke sanya dokar ta-baci don wanzar da zaman lafiya.