An kai hari a Coci a Burkina Faso
May 13, 2019Talla
Magajin garin mai suna Dablo ya ce 'yan bindigar ba su bar wurin ba, sai da suka cinnawa ginin da wasu shaguna da ke harabar cocin wuta, tare da kona motar wata jami'ar lafiya. Harin da aka kai a karshen mako ya haifar da rudani a tsakanin mazauna yankin. Makwanni biyu da suka gabata ma dai, 'yan bindiga a kan babura sun kai hari kan Cocin Pentecostal, inda suka hallaka limamin cocin da mabiyansa biyar. Burkina Faso na daga cikin kasashen yankin Sahel da ke fama da ayyukan mayakan jihadi.