Burkina Faso: Sojoji sun fatataki 'yan ta'adda
November 10, 2017Talla
Wani babban sojan kasar ta Burkina Faso ya sanar da wannan labari, inda ya ce sojojinsu biyar sun samu raunuka kuma daya daga cikinsu na cikin mawuyacin hali. Sojojin na Burkina Faso sun samu kwato makammai masu yawa da alburusai daga hannun maharan. Arewacin kasar ta Burkina Faso dai mai makwabtaka da kasar Mali da kuma Jamhuriyar Nijar, na fama da tarin matsalolin tsaro, inda wani adadi da hukumomin kasar suka bayar a farkon shekara ta 2015 ya nuna cewa 'yan jihadin sun kai hari har sau 80 da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 133 daga wannan lokaci zuwa farkon watan Nuwamba na 2017