1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso ta katse hulda da Taiwan

Gazali Abdou Tasawa
May 24, 2018

Kasar Burkina Faso ta sanar da katse huldar diplomasiyya da kasar Taiwan wannan kuwa duk da dinbin taimakon da kasar ke samu daga kasar ta Taiwan.

https://p.dw.com/p/2yGci
Burkina Faso Präsidentschaftswahlen Roch Marc Christian Kabore
Hoto: DW/K. Gänsler

Kasar Burkina Faso ta sanar da katse huldar diplomasiyya da kasar Taiwan wannan kuwa duk da dinbin taimakon da kasar ke samu daga kasar ta Taiwan. Ministan harakokin wajen kasar ta Burkina Faso Alpha Barry ne ya sanar da haka a wannan Alhamis inda ya ce gwamnatinsa ta dauki wannan mataki ne domin kare amfanin kasar Burkina faso da al'ummarta a kasashen duniya da kuma kulla hulda da kasashen da za su kasancewa  mafi tasiri da za su taimaka wa kasar ga bunkasa tattalin arzikinta da rayuwar al'ummarta.

Ministan ya ci gaba da cewa tuni ma shugaban kasa Roch Marc Christian Kabore ya ba shi umurnin daukar matakan gaggauta rufe ofishin jakadancin kasar tasa a Taipei da kuma na kasar ta Taiwan a Burkina. 

A shekara ta 1994 ne kasar ta burkina Faso ta kulla huldar diplomasiyya da kasar ta Taiwan. Dama dai kasashen Burkina Faso da Swaziland ne kadai kasashen Afirka da ba su katse huldar diplomasiyyarsu ba da kasar ta Taiwan. A jumulce a yau kasashe 18 ne kawai a duniya ke da huldar diplomasiyya da kasar ta Taiwan.