An nemi a kamo Blaise Campaore a ko'ina
December 21, 2015Talla
Kasar Burkina Faso ta gabatar da takardar sammaci ta kasa da kasa wacce ke bukatar a kama tubabben shugaban kasar Blaise Compaore, a kamun da ke da alaka da kisan tsohon shugaban kasar Thomas Sankara kamar yadda majiyar shari'a ta fada wa kamfanin dillancin labaran Reuters a ranar Litinin din nan.
Lauya da ke bangaren iyalan tsohon shugaban kasar ta Burkina Faso Thomas Sankara wato Prosper Farama, ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labaran Reuters wannan labari inda ya ce an sanya takardar sammacin ne ta kasa da kasa a kan shugaba Campaore a cewar alkali mai bincike.